Wata kotun Majistare a Bauchi ta ba da umarnin tsare wani fitaccen malamin addinin Musulunci na jihar, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a gidan yari.
Rundunar 'yan sandan jihar ce ta gurfanar da malamin mai janyo ka-ce-na-ce a gaban kotu ranar Litinin, bayan ta gayyace shi game da wani ƙorafi da aka shigar gabanta.
Matakin na zuwa ne sama da wata É—aya bayan Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Bauchi ta É—age wani zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda aka yi zargin ya furta wasu miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu.
Sai dai malamin da wasu masu goyon bayansa sun musanta zargin, suna cewa kalaman Sheikh Idris Dutsen Tanshi, ba munana lafazi ba ne ga Fiyayyen Halitta.
Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su É—auki mataki.
Lauyan malamin Barista Umar Hassan ya tabbatar da cewa an tsare Sheikh Idris Abdul'aziz, bayan sun nemi a bayar da belin sa, kuma kotu ta sanya Talata a matsayin ranar da za ta ba da hukunci a kan wannan buƙata.
0 Comments