A cewarsa mai shigar ƙara na 'yan sanda ne ya gabatar da tuhumar, inda kuma aka bai wa Sheikh Dutsen Tanshi dama, shi kuma ya tashi, ya musanta zargin da aka yi masa.
Barista Umar Hassan ya ce bayan an karanto wa malamin wannan tuhuma kotu ta tambaye shi, ko yana da dalilin da zai hana a hukunta shi?
"Sai ya ce, eh yana da dalilin da zai hana a hukunta shi. Wannan maganar da aka faÉ—a cewa ya tada hankalin al'umma, ba gaskiya ba ne".
Ya faɗi haka a gaban alƙali, in ji Bar Umar.
0 Comments